Jami’ar Maiduguri Ta Fitar Da Cut-Off Mark
Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta amince da maki 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar, a kakar karatu ta 2023/2024.
Inda kuma za ta buɗe shafinta domin fara rijistar Post-UTME, da Online Screening (Ga Ɗaliban DE), a ranar Litinin, 18 ga watan Satumban da mu ke ciki, ya yin da za a rufe, a tsakiyar daren Lahadi, 22 ga watan Oktoba.
Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Magatakardan Jami’ar Ahmad A. Lawan ya fitar, inda sanarwar ta ƙara da cewar, ɗalibai za su iya fara rijista daga waccar rana da aka ambata, ta hanyar garzayawa shafin: putme.unimaid.edu.ng.
Wajibi ne kuma, ga dukkannin ɗalibin da ke da sha’awar sayan Form ɗin Post-UTME ko Online Screening ɗin a Jami’ar ya sanyata, a matsayin zaɓinsa na farko (First Choice), tare da ɗora sakamakonsa na kammala Makarantar Sakandire (O’level), Wanda ya ƙunshi aƙalla Credits 5, da su ka haɗarda Lissafi da Turanci (Mathematics & English) a shafin hukumar JAMB.
Ga Ɗaliban DE kuwa, wajibi ne ya kasance su na da abinda bai gaza ‘Lower Credit’ ba a sakamakon su na Diploma ta ƙasa (ND) ko Babbar Diploma ta ƙasa (HND), ko kuma Merit a karatun NCE.
Muna yi muku fatan samun Nasara.
MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956