Ilimi

Jami’ar Najeriya Ta Janye Batun Rubuta Post-UTME, Saboda Matsin Tattalin Arziƙi

Hukumar gudanarwar Jami’ar Najeriya (UNN), da ke Nsukka, ta sanar da soke batun rubuta jarrabawar Post-UTME ta kakar karatu ta 2023/2024, da Jami’ar ta shirya rubutawa a watan Oktoba mai kamawa.

Post-UTME dai, jarrabawa ce da makarantu ke shiryawa, da nufin sake tantance Ɗalibai kafin basu guraben karatu, bayan sun samu nasara a Jarrabawar JAMB UTME.

Wannan cigaba kuma ya zo ne, ta cikin wata sanarwa da Magatakardan Jami’ar, Mrs C. N. Nnebedum ta fitar, a ranar Juma’a, ta na mai cewa hakan ya zo ne, sakamakon halin matsin tattalin arziƙi da ƙasar nan ta tsinci kanta.

Matsin wanda ya samo asali daga cire tallafin manfetur da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi, ana ganin ya jefa fannin sufurin ƙasar nan cikin halin ƙaƙanikayi, sakamakon nin-ninkawar da kuɗin mota ya yi.

Takardar sanarwar, ta kuma ƙara da bayyana cewar, hukumar gudanarwar Jami’ar ta ɗauki matakin soke rubuta jarrabawar ta Post-UTME ne, bayan duba da wahalhalun da Jama’a ka iya fuskanta, sakamakon tafiye-tafiye daga wuraren da su ke zaune, zuwa jihar ta Enugu.

A cewar Magatakardan kuma, Jami’ar za ta tantance sakamakon jarrabawoyin JAMB UTME, O’Level, da ma Direct Entry Results ɗin Ɗaliban da su ka nemeta ne, domin basu guraben karatu.

Sanarwar ta na cewa, “Ana sanar da dukkannin ɗalibai da sauran al’umma cewar, Jami’ar Najeriya, Nsukka ta fasa gudanar da jarrabawar Post-UTME da ta shirya gudanarwa, daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, zuwa Juma’a, 18 ga watan na Oktoban 2023.

“Hukumar gudanarwar wannan Jami’a ta ɗauki wannan mataki ne, domin rage wahalhalun Sufuri, da na muhallan kwana da ɗalibai za su fuskanta sakamakon halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

“Makaranta ta yanke shawarar cewa, kawai za ta tantance sakamakon jarrabawoyin JAMB UTME, O’Level, da Direct Entry Results ne, a madadin jarrabawar ta Post-UTME.

“Saboda haka, dukkannin ɗalibin da ya gaza Uploading ɗin sakamakonsa na O’Level a JAMB CAPS, a lokacin tantancewa, ba za a bashi gurbin karatu (Admission) ba”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button