Ilimi

Jami’ar Sule Lamiɗo, Kafin Hausa, Ta Fitar Da Cut-Off Mark Tare Da Ranar Fara Rijistar Post-UTME

Jami’ar Sule Lamiɗo, da ke Kafin Hausa, a Jihar Jigawa, ta amince da maki 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar, a kakar karatu ta 2023/2024, Inda ta shirya fara rijistar Post-UTME da Online Screening a gobe Litinin, 11 ga watan Satumba, zuwa tsakiyar daren ranar Litinin, 24 ga watan na Satumba.

Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar, mai lamba SLU/R/UAC/155/Vol.1, da ke ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Satumban 2023 miladiyya, dai-dai da 26 ga watan Safar, na shekarar 1445 bayan Hijirar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, daga garin Makkah zuwa birnin Madina.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewar, wajibi ne, dukkannin ɗalibin da ke neman gurbin karatu a Jami’ar ya kasance ya na da aƙalla Credits 5 a sakamakon jarrabawarsa ta kammala Sakandire, wanda ya haɗar da darussan Lissafi, da Turanci (Mathematics & English), ba ya ga sanya makarantar a matsayin zaɓin farko (First Choice) da shi ma ya kasance jazaman.

Dukkannin ɗaliban da su ka cika waɗannan sharuɗɗa kuma, za su iya neman Jami’ar ta hanyar adireshinta na ƴanar gizo, akan : www.slu.edu.ng, tare da cire Acknowledgement Slip, da shaidar biyan kuɗi (Evidence Of Payment).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button