Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano, Ta Sanya Ranar Bikin Rantsar Da Sababbin Ɗalibai
Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da ke birnin Kano, ta sanya ranar Laraba, 7 ga watan Yunin da mu ke ciki, a matsayin ranar gudanar da bikin rantsuwar sababbin ɗaliban Jami’ar, na kakar karatu ta 2022/2023.
Bayanin hakan na ɗauke ne, ta cikin wata sanarwa, da Jami’ar ta fitar, mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Yuni, wacce kuma aka aike ta ga ɗaukacin Shuwagabannin sassan Jami’ar.
Sanarwar dai, ta ce za a gudanar da bikin rantsar da Ɗaliban, tare da bayyana musu tsare-tsare da ma dokokin Jami’ar ne, a ɗakin taro na Farfesa Hafiz Abubakar, da ke sashen cikin birni (City Campus) na Jami’ar, da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar ta Larabar, makon da mu ke ciki.
Wannan sanarwa kuma, ta sanya zuƙatan Ɗaliban Jami’ar da dama waɗanda ke dakon wannan rana cikin annashuwa.
SAI MUN HAƊU, A CAN
✍️Miftahu Ahmad Panda.