Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Ta Tsawaita Wa’adin Rijistar Post-UTME
Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da ke birnin Kano, ta amince da tsawaita wa’adin lokacin rijistar Post-UTME, da Online Screening (Ga masu DE), zuwa ranar 6 ga watan Satumbar 2023.
Bayanin hakan na ɗauke ne, ta cikin wata sanarwa, da Shugaban sashen Adana bayanai (Registrar) na Jami’ar ya sanyawa hannu.
Inda sanarwar ta ce, an tsawaita lokacin da aka tsara rufe rijistar, daga ranar 27 ga watan Augustan 2023, zuwa 6 ga watan Satumba, Kuma a yanzu an tsara rubuta jarrabawar ta Post-UTME ne a ranakun Laraba 13 da Alhamis 14 ga watan Satumbar 2023 (cikin kwanaki 2), a sashen Makarantar da ke Titin Ƙofar Ruwa.
Su kuwa masu neman Makarantar ta hanyar D.E, za a tantance su (Screening) ne, a ranakun Juma’a 15 da Asabar 16 ga Watan Satumbar da mu ke ciki, a Sassan da su ka nema (Departments), da ke rassan Makarantar guda biyu.
✍️Miftahu Ahmad Panda (Computer Science Department) – YUMSUK.
08039411956