Ilimi

Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Za Ta Zama Jagora A Fannin Bincike – Abba Gida-Gida

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Jami’ar Yusuf Maitama Sule, mallakin Gwamnatin Jihar, za ta kasance daga cikin Jami’o’in da ke Jagorantar manya-manyan bincike, a nan gaba kaɗan.

Hakan kuma na ɗauke ne ta cikin wani jawabi, da Jami’in yaɗa labaran Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar, Malam Sunusi Kofar-Na’isa ya fitar, ranar Lahadi, a birnin Kano.

Gwamna Abba, wanda kuma ya ke a matsayin “Visitor” na Jami’ar, ya bayyana hakan ne a ya yin wata ziyara da ya kai Jami’ar.

Gwamnan, wanda Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar-Mata ya wakilta, ya bayyana cewar za a cimma hakan ne ta hanyar duba ɗumbin nasarori da ababen tarihin da Jami’ar ta cimma, Jajirtattun Ma’aikata (Masu Koyarwa ba waɗanda ba Malamai ba), da ma kyakykyawan tsarin Shugabancin da ta ke da shi.

Gwamnan, ya kuma buƙaci Shuwabanni, Ma’aikata (Malamai Da Waɗanda Ba Malamai Ba) da su cigaba da Aiki tuƙuru a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya, dan ganin an cicciɓa Jami’ar zuwa matakin nasara.

Ka zalika, ya kuma ce zai haɗa hannu da dukkannin hukumomin da abin ya shafa, wajen ganin an gudanar da wannan Aiki, ta hanyar fara kammala Ayyukan da aka fara gudanarwa a Jami’ar.

Bugu da ƙari, ya kuma ce, Gwamnatinsu za ta bawa Jami’ar dukkannin wata gudunmawa, dan ganin ta riski matakin da za a dinga yin gogayya da ita, a matakin Duniya.

“Idan mu ka duba Logon wannan Jami’a, za mu ga yana nuna yankin Arewa Maso Yamma ne, duk da cewar dai an sauya sunan Jami’ar, Amma idan mu ka duba Logo ɗinta, za mu ga har yanzu hoton yankin Arewa Maso Yamma ya na nan.

“Kuma manufar samar da Jami’ar da, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi, shi ne Haɗa Kai, Da farfado da martabar yankin Arewa Maso Yamma, ta fuskar Ilimi.

“Amma son zuciyar Gwamnatin da ta gabata, ya sa ta dinga yanke Filin Jami’ar da wasu kadarorinta ta na sayarwa; Kuma dukkanninmu mun sani, hatta sauya sunan Jami’ar ma gilli ne kawai na Siyasa, wanda ya bi ta kan yunƙurinmu na fifita buƙatar yankin”, a cewarsa.

A jawabinsa tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya ce ziyarar za ta kasance tamkar wani magani, na kawo ƙarshen matsalolin Jami’ar, bayan da ya bayyana ƙwarin guiwarsa ga yunƙurin Gwamnati mai ci ta fuskar bunƙasa Ilimi.

A nasu ɓangaren, ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’ar, buƙatar Gwamnatin su ka yi da ta dawowa da Jami’ar kadarorinda da aka cefanar na Kwanar Dawaki, tare da ƙara kuɗaɗen alawu-alawus ɗin membobinsu na ƙarshen wata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button