Jaruma Khadija Mai Numfashi Ta Yi Nadama, Ƙasa Da Mako Biyu Bayan Dakatar Da Ita Daga Kannywood
Fitacciyar Jaruma a masana’antar Kannywood, wacce ludayinta ke kan damo, Khadija Kabir Ahmad, wacce aka fi sani da Khadija Mainumfashi, ta bayyana laɗama kan abin da ta aikata, ƙasa da mako biyu, bayan da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin, Abba El-Mustapha ta dakatar da ita, daga masana’antar shirya fina-finan Hausa, na tsawon shekaru biyu.
Mainumfashi ta bayyana nadamarta ta ne, ta cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa, a shafinta na kafar sada zumunta ta TikTok.
Idan ba a manta ba dai, hukumar tace fina-finai ta dakatar da jarumar daga Kannywood ne, bayan fitar bidiyo da ke nuna yadda take raƙashewa cikin salon rawar solo – samfurin uwa ba gwaɓa, inda kuma bayan cece-kucen da faifan bidiyon ya haifar ne, hukumar tace fina-finai ta Kano ta gayyaci jarumar, domin jin ta bakinta, amma ta yi kunnen uwar shegu da gayyatar, lamarin da ya fusata shuwagabannin hukumar, har su ka ɗauki matakin dakatar da ita.
A bidiyon da ta wallafa, ranar Alhamis dai, Jaruma Mainumfashi ta nemi afuwar hukumar ta tace fina-finai, tare da dukkannin mutanen da basu ji daɗin abin da ya faru ba, ta na mai cewar – itama kanta bata ji daɗin abin da ta aikata ba, a cikin bidiyon nata wanda ya bayyana.