Jarumar Film Na Shirin Garzayawa Kotu, Bayan Ɓullar Bidiyon Tsaraicinta
Jaruma a masana’antar shirya fina-finan kudancin Najeriya (Nollywood), Moyo Lawal, ta yi martani kan wani fai-fan bidiyon tsaraicinta, da ke yawo a Shafukan Sada Zumunta, a jiya (Asabar).
Bidiyon wanda ya nuna jarumar ta na saduwa da wani Namiji, a yanzu dai baki ya karkata kan cewar tsohon Saurayinta ne, ya na shan doguwar tattaunawa a kafafen sada zumunta na zamani, inda mutane da dama ke zargin cewar Jarumar ta saki bidiyon ne kawai da kanta.
Sai dai, da ta ke martani, a shafinta na Instagram, a ranar Lahadi, Jaruma Moyo, ta tabbatar da cewar ita ce a cikin bidiyon, kafin kuma ta musanta cewar ita ta saki, tare da yaɗa bidiyon.
“An saki bidiyon tsaraicina na wani lokaci da ya gabata, ba tare da sanina ba, wanda hakan ya bayyanar da sirrina da gaskiyata”, a cewar jawabin.
“Ina son sanar da ku cewar, mun yi wannan bidiyon ne da tsohon Mijina, wanda da zan Aura a wancan lokacin, amma ban yi shi dan Jama’a su gani ba, kuma bani na sake shi ba. Dan haka zan ɗauki matakin Shari’a kan bayyanar wannan sirri nawa”., ta ƙarƙare jawabinta.