Jarumar Nollywood Ta Musulunta
Jaruma a masana’antar shirya fina-finan kudancin Najeriya, Mercy Aigbe, ta sanar da cewar, ta koma Addinin Musulunci, inda ta bayyana sabon sunanta, a ya yin wani taron faɗakarwa, da addu’o’i na musamman na watan Ramadan wanda ita da Mijinta, Kazeem Adeoti, su ka ɗauki nauyin gudanarwa, a ranar Asabar.
Ta cikin faifan bidiyon da aka fitar a ranar Lahadi dai, an hango inda jarumar ke cewa, ”Insha’Allah!, Sabon sunana shi ne Hajiya Meenah Mercy Adeoti. Wato Meenah mai H.”.
Hakan kuma, na daga cikin ƙaruwar da Addinin Musulunci ke cigaba da samu, musamman ma a ya yin wannan wata mai tarin falala na Ramadan.
Addu’ar Rariya Online dai ita ce, Allah ya cigaba da ɗaukaka darajar Addinin Musulunci da Musulmai, Albarkacin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.