Jerin Ƴan Najeriya 40 Da Ke Da Jiragen Hawa Na Kansu, Tare Da Tarin Dukiyar Da Su Ka Mallaka
Mallakar jirgin hawa na ƙashin kai a Najeriya, ba isa kawai ya ke nunawa ba, a’a ya na kuma ƙara fito da tarin arziƙin da mamallakin wannan jirgi ya ke da shi, duba da yadda wasu daga cikin ƴan Najeriya, musamman ƴan siyasa, ƴan masana’antar nishaɗi, da ma ƴan kasuwa, ke da mallakin jiragen hawan nasu na kansu.
AMB ta rawaito cewar, kowanne jirgin hawa na ƙashin kai, ya na laƙume aƙalla tsakanin Dalar Amurka 500,000 zuwa 1,000,000 (kwatankwacin Naira 290,000,000 zuwa 580,000,000), amma har yanzu wasu daga cikin masu farcen susa, su na cigaba da mallakarsa, duk da wannan tsadar da ya ke da ita.
Kula da jirgin ma, ba ƙaramin aiki bane, duba da tarin ɓangarorin da ake lura da su kowanne lokaci, kamar ‘C’ checks, software checks, matakin mai (fuel level), kafin tashi, bayan sauka, da kuma binciken mako-mako.
Ire-iren jiragen hawan kuma sun haɗar da: Very Light Jets, Light Jets, Mid-Size Aircraft, Super Mid-Size Jets, Heavy Business Jets, Ultra-long range jets, da Executive Airliners.
Ga jerin wasu ƴan Najeriya, da ke da mallakin jiragen hawa na ƙashin kansu, tare da yawan arziƙin da su ke da shi :
1• Aliko Dangote – Shugaban Dangote Group – Dala biliyan 19.6.
2• Mike Adenuga – Shugaban Globacom Ltd – Dala biliyan 7.
3• Allen Onyema – Shugaban Airpeace – Dala biliyan 3.1.
4• Arthur Eze – Shugaban Atlas Oranto Petroleum – Dala biliyan 5.8.
5• Igho Sanomi – Ɗan Kasuwa– Dala biliyan 1.
6• Adedeji Adeleke – Mamallakin Jami’ar Adeleke – Dala miliyan 700.
7• Cletus Madubugwu Ibeto – Shugaban The Ibeto Group – Dala biliyan 3.8.
8• Apostle Johnson Suleman – General overseer Na Babbar Ma’aikatar Lantarki – Dala miliyan 10.5.
9. Dr. Bryant (ABC) Orjiako – Shugaba, kuma wanda ya samar da SEPLAT – Dala biliyan 1.2.
10• Femi Otedola – Ɗan Kasuwa – Dala biliyan 1.2.
11• Orji Uzor Kalu – Ɗan Siyasa kuma Ɗan Kasuwa – Dala biliyan 1.1.
12• Late Prophet TB Joshua – General overseer SCOAN – Dala miliyan 15.
13• Bishop David Oyedepo – General overseer na Cocin Living Faith – Dala miliyan 200.
14• Joseph Arumemi-Ikhide – Wanda ya samar da Arik Air – Dala biliyan 3.
15• Theophilus Danjuma – Ɗan Siyasa– Dala biliyan 1.1.
16. Pastor Adeboye – General Overseer na Cocin Redeemed Christian Church of God – Dala miliyan 65.
17• Pastor Ayo Oritsejafor – Tsohon Shugaban Ƙungiyar Kiristoci Ta Ƙasa – Dala miliyan 32.
18• Folorunsho Alakija – Ƴar Kasuwa – Dala biliyan 1.53.
19• Ibrahim Badamasi Babangida – Tsohon Janar Mai Ritaya – Dala biliyan 5.
20• Atiku Abubakar – Ɗan Siyasa – Dala biliyan 1.8.
21• Olusegun Obasanjo – Ɗan Siyasa– Dala biliyan 1.6.
22• Rochas Okorocha – Ɗan Siyasa – Dala biliyan 1.4.
23• Rotimi Amaechi – Ɗan Siyasa– Dala miliyan 780.
24• Sanata Ali Modu Sheriff – Ɗan Siyasa – Dala miliyan 1 – Dala miliyan 5.
25• Godswill Akpabio – Ɗan Siyasa – Dala miliyan 20.
26• Obi Cubana – Ɗan Kasuwa – Dala miliyan 96.
27• Tiwa Savage – Mawaƙi – Dala biliyan 17.
28• Phyno – Mawaƙi – Dala miliyan 12.
29• Ned Nwoko – Ɗan Siyasa kuma Ɗan Kasuwa – Dala biliyan 1.2.
30• Jide Omokore – Ba a gano adadin kuɗi ba.
31. Pastor Chris Oyakhilome – General Overseer na Christ Embassy – Dala miliyan 50.
32• Prophet Jeremiah Omoto Funfeyin – Shugaba a Christ Mercyland Deliverance Ministry – Dala miliyan 35.
33• Wizkid – Mawaƙi – Dala miliyan 30.
34• Don Jazzy – Mawaƙi – Dala miliyan 10.
35• Patrick Ifeanyi Ubah – Ɗan Siyasa– Dala biliyan 1.7.
36• Jimoh Ibrahim – Ɗan Kasuwa– Dala biliyan 1.1.
37• DJ Cuppy – DJ – Dala miliyan 3.
38• Ernest Azudialu Obiejesi – Ɗan Kasuwa– Dala miliyan 900.
39• Olamide – Mawaƙi – Dala miliyan 12.
40• P-Square – Mawaƙi – Dala miliyan 100.