Ilimi

Jigawa Polytechic Ta Fitar Da Cut-Off Mark

Hukumar gudanarwar Jigawa State Polytechic, Dutse, na sanar da dukkannin ɗaliban da su ke da sha’awar neman Makarantar a kakar karatu ta 2023/2024 cewar ta fara sayar da Form ɗin Post-UTME ga ɗaliban da su ka cika waɗannan sharuɗɗan :

•Wajibi ne ɗalibi ya sanya Polytechic ɗin ta Jigawa a matsayin zaɓinsa na farko (First Choice).

•Wajibi ne ya samu mafi ƙarancin makin shiga Polytechic, a jarrabawar UTME ta 2023 da ta gabata.

•Wajibi ne ɗalibi ya ɗora (ya yi Uploading) ɗin sakamakonsa na kammala Sakandire, a shafin hukumar JAMB (JAMB CAPS).

GA JERIN KWASA-KWASAN DA MAKARANTAR TA KE YI :

ND in Accountancy.

ND in Business Administration.

ND in Public Administration.

ND in Office Technology.

ND in Social Administration.

ND in Architecture.

ND in Building Technology.

ND in Electrical and Electronics.

ND in Quantity Surveying.

ND in Welding and Fabrication.

ND in Civil Engineering.

ND in Mechanical Engineering.

ND in Estate Management.

ND in Urban and Regional Planning.

ND in Computer Science.

ND in Science Laboratory Technology.

ND in Statistics.

ND in Environmental Health.

ND in Leisure & Tourism Management.

ND in Nutrition & Dietetics.

ND Social Administration.

ND Office Technology.

YADDA AKE CIKEWA :

Duk ɗalibin da ya ke da sha’awa zai halarci adireshin : https://jigpoly.admissions.cloud/ , Sai ya yi Generating Invoice, Ya kuma garzaya banki domin biyan Naira 5,500 a matsayin kuɗin Form.

_Sannan ya koma zuwa shafin, domin cike sauran bayanansa.

KU SANI :

Dukkannin wani bayani da ku ka canja bayan kun tura (After Submission), ba zai sauyu ba, har sai kun je MIS na Polytechic ɗin kun biya Naira 1,000.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button