Siyasa
Jonathan Ya Kai wa Ganduje Ziyara
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya kai wa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ziyara, a gidansa, da ke babban birnin tarayya Abuja.
Bayanin kai ziyarar tasa kuma, na ɗauke ne ta cikin wasu hotuna da aka wallafa a shafin X na jam’iyyar ta APC, da safiyar ranar Juma’a.
Inda aka rubuta, “Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, #GEJonathan a gidansa, da ke babban birnin tarayya Abuja “.
Sai dai, har ya zuwa yanzu, babu bayani kan abubuwan da shuwagabannin su ka tattauna a ya yin wannan ziyara.