Siyasa

Ka Yi Wa Ƴan Ƙasa Bayanin Yadda Ka Shiga Jami’a, Ba Tare Da Karatun Sakandire Ba – Buƙatar Atiku Ga Tinubu

Ɗan takarar Shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, a zaɓen 2023 da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya yi wa al’ummar Najeriya bayanin yadda ya samu gurbin karatu a Jami’ar Jihar Chicago, ba tare da takardun shaidar kammala Makarantun Firamare da Sakandire ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar, ya kuma bayyana hakane ta shafinsa na Sada Zumunta, da yammacin ranar Lahadi.

Atiku, wanda a yanzu haka ya ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, ya ce ya gaza fahimtar iƙirarin yin karatun da Shugaban ƙasa, Bola Tinubun ke yi.

Inda ya bayyana shakkunsa ƙarara kan yadda Tinubu ya mallaki shaidar kammala karatun Digiri, daga fitacciyar Makaranta kamar Chicago, ba tare da yin karatun Firamare da Sakandire ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button