Tsaro

Kaduna: Jama’ar Tunburku, Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Rashin Tsaro

Al’ummar kauyen Tunburku, da ke mazabar Kidandan din karamar hukumar Giwa, ta jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana, dan jan hankalin mahukunta kan yawaitar garkuwa da mutane da ayyukan yan bindiga da su ka addabi yankin.

Dubban masu zanga-zangar wadanda su ka hadarda matasa da tsofaffi sun gudanar da zanga-zangar ne, Masarautar Zazzau, da ke Zaria.

Jagoran masu zanga-zangar, Malam Yusuf Jibrin, a ce sun damu matuka kan hare-haren da yankin ya ke fuskanta akai-akai, ya na mai karawa da cewar, ayyukan yan bindiga da sauran miyagun ayyukan da su ka addabi yankin ba abu ne da za su lamunta ba. Yusuf, ya ce ayyukan yan bindigar sun gurgunta harkokin noma da sauran bangarorin tattalin arzikin jihar, ba ya ga gurgunta zaman lafiya da hakan ya haifar.

Shi ma wani mazaunin kauyen na Tunburku, Amiru Abubakar, ya bayyanawa Sarkin cewar, yan bindiga na hallakawa tare da sace mazauna yankin, inda a wasu lokutanma ba sa bari a yi noma, har sai an biya su kudin fansa. Inda ya ce da tsakar rana su ke shiga yankin su sace musu dabbobinsu, ya yin da su ke mu’amalantarsu kamar bayi. A jawabinsa ga masu zanga-zangar, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce Dagacin kauyen na sanar da matsanancin hali da ake ciki ga Masarautar akai-aikai, ya na mai cewar halin da karamar hukumar ta Giwa ke ciki ya na hana su barcin dare.

Inda ya koka da halin ta’azzarar matsalolin tsaron, tare da kira ga hukumomin da abin a shafa kan su yi abin da ya dace.

Ya kuma bayyanawa mutanen cewar, ya sanar da Gwamnan jihar halin da ake ciki, a ya yin taron kwamitin tsaro da aka gudanar.

Inda ya roki mutanen da su kasance masu hakuri, ya yin da gwamnati ke yunkurin sake jibge jami’an tsaro, a yankin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button