Kimiyya Da Fasaha

Kamfanin Google Zai Goge Gmail Accounts Ɗin Da Aka Daina Amfani Da Su

Kamfanin Google, ya bayyana aniyarsa ta goge dukkannin asusan tura saƙonni na Gmail ɗin da aka daina amfani da su, a ranar 1 ga watan gobe na Disamba.

Ta cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa, ya bayyana cewar, zai goge Gmails Accounts ɗin ne idan ya kasance sun kai tsawon shekaru biyu, ba a shiga (Login), ko aiwatar da wani aiki da su ba.

Ayyukan da kamfanin zai duba, domin tantance Gmail ya na aiki, ko akasin hakan dai, sun haɗarda shiga Asusun (Signin); Karantawa ko aikewa da saƙo; Amfani da ma’adanar Google Drive; Kallon Fina-Finai a YouTube; Tura Hotuna; Sauke Manhajoji; da ma bincike a Injinan bincike na Search Engines, ya yin da asusun ya ke kan na’urar da ake gudanar da aikin.

Kamfanin ya kuma ce, a ranar ta 1 ga watan Disamba, zai fara ne da goge Accounts mafiya daɗewa.

Tsarin kuma, zai shafi Asusun Mallakin Kai (Personal Accounts) ne kaɗai, ban da na kamfanoni, makarantu, ko hukumomi.

“Kamfanin Google ya na da damar goge bayananku, muddin ku ka shafe tsawon shekaru 2, ba ku yi amfani da Asusun ba”, a cewar saƙon.

“A ranar 1 ga watan Disamba, za a goge Accounts ɗin da lamarin ya shafa, saboda wannan tsari “.

Ka zalika, akwai wasu dalilai da ka iya dakatar da kamfanin na Google daga goge Asusun mutum, kamar: Idan an yi amfani da asusun wajen sayen wani abu a Google Playstore; ko kuma Asusun da ke da gift card mai balance a cikinsa.

Google ya kuma ce, zai sanar da masu amfani da Accounts ɗin, ta hanyar aike musu da saƙonnin emails ga asusan nasu, ko kuma recovery emails ɗin da su ka saka.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button