Labarai

Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen Sama Na Ƙasa, Zai Fara Aiki Kafin Saukar Buhari

Ya yin da ya rage ƙasa da makonni huɗu, a rantsar da sabuwar gwamnati, a ranar Laraba, Ministan sufurin jiragen sama na ƙasa, Hadi Sirika, ya sake jaddada cewar, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa, zai fara aiki, kafin ko a ranar 29 ga watan Mayu.

Ministan ya bayyana yadda gwamnati ta mayar da hankali kan aikin ne, a ya yin da ya ke zantawa da manema labaran fadar shugaban ƙasa, kan abubuwan da aka tattauna a ya yin taron majalissar zartarwa ta ƙasa, da ya gudana ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja.

”Ina tunanin ai makonni uku lokaci ne wadatacce. Da yardar Allah jiragenmu za su fara tashi. Ka da kuma ku manta ai ba yau muka fara ba. Mun fara wannan aiki ne, tun 2015”, a cewar Sirika.

Ministan ya kuma yi bayanin cewar, sun samar da tsari tare da taswirar aikin, da ma tattaunawa da masu bayar da shawarwari ne, tun a shekarar 2016.

Inda kuma aka ƙaddamar da Aikin, a ƙasar Ingila, a ranar 18 ga watan Yulin 2018.

Ana kuma sa ran Aikin zai laƙume kimanin Dalar Amurka miliyan 308.8.

An kuma fara tunanin samar, da tsarin sufurin na ƙasar nan ne tun tsawon shekaru, bayan da kamfanin da ake da shi a baya (Nigeria Airways) ya durƙushe, sakamakon rashawa, da ma gaza kulawa da shi.

A watan da ya gabata ne kuma, Hadi Sirikan ya alamta cewar, sabon tsarin sufurin jiragen saman na ƙasar nan, zai fara aiki, kafin rantsar da sabuwar gwamnati, a ranar 29 ga watan Mayu.

”Zai fara gudanar da aiki a cikin ƙasa, da ma ƙasa da ƙasa nan kusa. Kafin ƙarewar zangon gwamnatin nan, a ranar 29 ga watan Mayu, za mu tashi”, a cewar Sirika.

Ya na mai ƙarawa da cewar, ” a yanzu haka ana tsaka da tattaunawa da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopian Airlines.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button