Kano: Alhaji Sani Ya Buƙaci A Naɗa Amdaz Shugabancin HISBAH
Mai sharhin nan kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya buƙaci Gwamnatin Kano, da ta naɗa shahararren Mawaƙin nan, kuma Jarumi a Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, a matsayin shugaban hukumar HISBAH ta jihar.
Alhaji Zanginan ya ce, akwai buƙatar naɗa Amdaz ɗin kan wannan muƙami, muddin dai cigaba ake so, da gyaran al’umma.
“Toh ai sai ayiwa Abdallah Amdaz shugaban hisbah kawai indai son cigaban akeso da gyaran Al Umma.
“Allah yasama ya amince ya karba.”, a cewarsa.
Idan ba a manta ba dai, a jiya ne, shahararren Malamin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana murabus ɗinsa daga Shugabancin hukumar ta HISBAH, bayan da ya zargi gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da furta wasu kalamai da ya ce sun sace masa guiwa.
Al’umma da dama kuma, sun zargi Gwamnan da furta kalaman ne, sakamakon gurfanar da fitacciyar tauraruwar TikTok ɗin nan, Murjanatu Ibrahim Kunya, da hukumar ta yi a gaban Kotu, duba da cewar, bai taɓa sanya baki kan ayyukan hukumar ba, a baya.