Kano: An Daƙume Mutane 3 Bayan Yunƙurin Tada Hargitsi A Kasuwar Magani
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana yadda ta yi nasarar daƙume mutane uku, bayan da su ka yi yunƙurin tada zaune tsaye a kasuwar sayar da magunguna da ke jihar Kano, ya yin da masu sana’ar ke ƙoƙarin kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwar da gwamnatin jihar ta gina.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Hussaini Gumel, shi ne ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) lamarin, ranar Lahadi, a birnin Kano.
Gumel ya kuma ce, lamarin ya faru ne a Mai-Karami Plaza, ya yin da manyan ƴan kasuwar ke kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwar Dangwauro.
Kwamishinan ya kuma ce, ɓata garin sun yi yunƙurin tayar da hargitsi ne, domin samun damar afkawa wasu shagunan kasuwar da nufin aikata ɓarna.
Tuni kuma aka Jibge ɗumbin Jami’an ƴan sanda a Plazar, domin tabbatar da tsaro, ba ya ga tsare waɗanda ake zargin da aka yi.