Kano: An Gano Yarinya Ƴar Shekara 13, A Jerin Ma’aikatan Da Gwamnatin Ganduje Ta Ɗauka
Bayan shafe tsawon watanni da dakatar da sababbin ma’aikatan jihar Kano da guda 10,000 da Gwamnatin Ganduje ta ɗauka, tare da tantance su, da yanzu Gwamnatin ta Kano ƙarƙashin Jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta ce ma’aikata 9,332 ne su ka tsallake tantancewar sahihanci.
Da ya ke sanar da abin da kwamitin tantancewar ya gano, shugaban kwamitin wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya ce tuni aka amince da tura ma’aikatan da aka tabbatar da sahihancin ƙwarewar tasu, zuwa ma’aikatu daban-daban.
A jawabin, na Sakataren Gwamnatin Kano, da safiyar yau (Juma’a), ya ce akwai buƙatar mutane su sani cewar, daga cikin ma’aikatan da Gwamnatin Gandujen ta ɗauka ba bisa ƙa’ida ba, har da yarinya ƴar shekara 13, wanda hakan abu ne da ya ci karo da dokokin aikin Gwamnati.
Sauran kura-kuran da Baffa Bichin ya ce sun gano, sun haɗarda: ɗaukar waɗanda basu kammala hidimar ƙasa ba; da ɗaliban manya da ƙananan makarantun Sakandire; sai kuma ma’aikatan da aka sanya a ma’aikatun da basu dace da su ba, ta hanyar shan ban-ban da takardun karatu, ko ƙwarewarsu.
Idan ba a manta ba dai, Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta dakatar da sababbin ma’aikatan jihar, kimanin 12,566 da Gwamnatin Ganduje ta ɗauka, ya yin da take bankwana da mulkin jihar Kano, bisa zargin tafka badaƙala a cikin tsarin ɗaukar tasu.