Kano: Kotu Ta Haramtawa Hukumar Muhuyi, Binciken Bidiyon Dala
Babbar Kotun Tarayya, da ke Kano, ta yi hukuncin cewar, hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, ba ta da hurumin bincikar faifan bidiyon da ya nuna yadda tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ke sunƙuma daloli a aljihu.
Da ya ke yanke hukunci a ranar Litinin, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya ce laifin ya faɗa cikin dokar tarayya ne, saboda haka hukumar da ke a matsayin mallakin jiha, ba ta da ƙarfin gudanar da binciken.
Idan za a iya tunawa dai, tsohon Gwamnan jihar ta Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya maka hukumar ta Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar a gaban Kotu ne, ya na roƙon Kotun da ta dakatar da hukumar daga bincikar bidiyon da ke fito da zargin da ake masa da cin hanci da rashawa.
Zuwa yanzu kuma, tuni Lauyan wanda ake ƙara na farko, ya bayyana cewar za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.