Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Jingine Hukuncin Kotun Baya, Tare Da Umartar Gawuna Ya Biya Abba Tarar Miliyan 1
Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta umarci ɗan takarar Gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya biya, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP tarar Naira miliyan 1, bayan da ta yi watsi da ƙarar da Abban ya ɗaukaka.
Umarnin Kotun ɗaukaka ƙarar ya fito ne, ta cikin kwafin hukuncin da ta fitar a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan ƙarar da Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP ya shigar gabanta, ya na ƙalubalantar hukuncin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar ta zartar, wanda ya bawa, Nasiru Yusuf Gawuna nasara.
Kotun ɗaukaka ƙarar dai, ta yanke hukuncin nata ne, a ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, inda ta jingine hukuncin da Kotun sauraron shari’ar zaɓen Kanon ta yi, sai dai ta sake jaddada nasara ga Nasiru Yusuf Gawuna, na APC, bayan kafa hujja da cewar, Abba Kabir Yusuf ɗin ba sahihin ɗan jam’iyyar NNPP bane, a lokacin da aka tsayar da shi takara, kuma baya cikin rijistar membobin jam’iyya.
Kotun farko kuwa, ta ƙwace nasarar da Abba ya samu ne, bayan soke wasu ƙuri’u sama da 165,000 daga cikin ƙuri’un ɗan takarar na NNPP, bisa hujjar rashin sanya hannun jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da Sitamfin hukumar.