Kano State Polytechic Ta Fitar Da Cut-Off Mark, Tare Da Sanya Ranar Fara Sayar Da Form
Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano (Kano State Polytechic), ta sanya ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, a matsayin ranar da za ta fara sayar da Online Application Form ɗinta, ga Ɗaliban da ke da sha’awar neman guda daga cikin rassanta, guda biyar, a kakar karatu ta 2023/2024.
Ɗaliban da ke da sha’awa, kuma su ka samu aƙalla maki 100 a jarrabawar JAMB UTME ta shekarar 2023 dai, za su iya neman Makarantar, a matakin karatu na Diploma ta ƙasa (ND), Takardar Shaidar Ƙwarewar Malanta (NCE), da ma babbar Diploma ta ƙasa (HND), bayan sanya makarantar a matsayin zaɓukansu na farko (First Choices).
Jerin Makarantun da Ɗalibai za su iya nema, ƙarƙashin Kano State Polytechic Technic ɗin, sun haɗar da: School Of Technology (SOT), da ke kan titin Matan Fada, a birnin Kano; School Of Management Studies (SMS), da ke kan titin Yahaya Gusau; School Of Rural Technology & Entrepreneurship Development, da ke Rano; School Of Environmental Studies (SES) da ke Gwarzo; da School Of General Studies (SGS).
KU SANI : Ba dukkannin kwasa-kwasan ne ake buƙatar maki 100 ba, akwai masu maki 100, 110, 120, har ma da 140.