Kano: Wani Mutum Ya Kashe Mijin Ƴar Uwarsa, Akan Gishirin 20
Ana zargin wani mutum mai suna, Magaji Salisu, da hallaka wani magidanci, mai shekaru 45 a duniya, Zakari Hamza, wanda miji ne ga ƴar uwarsa, da ke Aure a Kano, bayan da su ka samu saɓani akan gishirin Naira 20.
Bayanin yadda lamarin ya faru, ya fito ne ta bakin ɗan mamacin mai suna, Ibrahim Zakari, wanda ya ce saɓanin da aka samu ne, ya yi sanadiyyar rasa ran mahaifinsa.
Ibrahim, ya ce rikicin ya fara ne yayin da Mahaifinsa ya dawo daga kasuwa, kuma matarsa mai suna, Sadiya Salisu, ta sanar da shi cewar, ta karɓo bashin gishiri na Naira 20, wanda kuma hakan ya ɓata ran mahaifin nasa matuƙa, sakamakon hana karɓar kowanne irin nau’in bashi da ya yi, ko da kuwa daga wanene.
Hakan ne kuma ya sa, mutumin ya koma shagonsa, tare da kiran ɗan uwan matarsa a waya, yana mai shaida masa abin da ya wakana tsakaninsa da matar tasa.
Hakan ne kuma ya ɓata wa ɗan uwan matar rai, ya bazama zuwa gidan, ya na kururuwar neman mijin ƴar uwartasa, amma bai same shi a gida ba, wanda hakan ya sanya ya bishi shagonsa da ke, Ƴan Shinkafa, a ƙaramar hukumar Kura.
Ɗan mamacin ya kuma bayyana cewar, bayan isar mutumin ne, sai ya fara dukan mahaifin nasa, wanda har sai da ya karya masa ƙasusuwan haƙarƙari.
Wanda hakan ya sanya suka ɗauke shi zuwa Asibiti mafi kusa da su, da ke garin Kura, inda Likitoci su ka kula da lafiyarsa, har zuwa lokacin da aka sallame su, wanda bayan komawarsu gida ne, mahaifin nasa ya rasu.
Ibrahim, ya kuma ce sun shigar da ƙorafin lamarin ga ofishin rundunar ƴan sanda, kuma tuni Baturen Ƴan Sanda na ƙaramar hukumar Kura ya gayyaci Matar, da Ɗan Uwanta, a yanzu haka ma su na tsare a hannunsu.
Ka zalika, ya yi kira ga Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, da ya tabbatar da an samarwa mahaifinsa adalci.
Har zuwa lokacin da mu ke haɗa wannan rahoto kuma, rundunar ƴan sanda bata ce komai game da lamarin ba.