Kotu

Kano: Yadda Rashin Kulawa Ya Sanya Kotu Kashe Auren Shekaru 14

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Kotun shari’ar Musulunci, a Kano, ta kashe Auren wani Direba mai suna, Zakari Ghali, da Matarsa, Shamsiyya Haruna, sakamakon rashin kulawa.

Ta cikin ƙunshin ƙarar da Shamsiyya, wacce ke zaune, a Unguwa Uku, da ke birnin Kano, ta shigar a gaban Kotu, ta roƙi Kotun da ta kashe Aurenta, tare da bata damar riƙe Ƴaƴanta, tana mai tawassali da yadda Mijin nata mai suna, Ghali ya yi watsi da ita, tare da yaransu guda biyar da su ka haifa, ba tare da basu abinci ba.

Da ya ke zartar da hukunci, Mai Shari’a Malam Umar Lawal-Abubakar, ya ce kotu ta kashe Auren ne, bayan dukkannin wani yunƙuri na sasanta Ma’auratan ya ci tura.

Kotun ta kuma umarci Ghali ɗin, da ya dinga bawa tsohuwar Matar tasa Naira 90,000 kowanne wata, a matsayin kuɗin kula da ƴaƴansu, da ke wurinta.

Ghali, ya bayyanawa Kotun cewar, ya bar gida ne, sakamakon halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

“Ba ni da kuɗin da zan kula da Iyalaina a yanzu. Mai motar da nake jigilar kayayyaki domin rufawa kaina asiri, ya karɓe abarsa,” a cewar Ghalin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button