Kano: Yadda Saukar Daurawa Daga Shugabancin HISBAH Ya Yamutsa Hazo
Saukar fitaccen Malamin nan ɗan asalin jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, daga shugabancin hukumar HISBAH ta jihar, sakamakon wasu kalamai da Gwamna, Abba Kabir Yusuf ya furta, waɗanda Malamin ya ce sun sakar masa da guiwa, a ranar Juma’ar da ta gabata, 1 ga watan Maris ɗin 2024, na cigaba da yamutsa hazo, tare da samun martani iri-iri daga mabanbantan mutane, a kafafen sada zumunta.
Al’umma da dama dai, sun zargi Gwamnan da sukar ayyukan Hisbah ne, sakamakon gurfanar da fitacciyar tauraruwar TikTok ɗin nan, Murjanatu Ibrahim Kunya, da ta yi, duba da yadda bai taɓa cewa ko da ‘ta tafasa’ ba kan ayyukan hukumar a baya.
Daga cikin masu martanin kuma, har da fitaccen Ɗan Jaridar nan, mamallakin Jaridar Yanar Gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, wanda ya zargi Gwamnan da gaza bawa na kusa da shi fuskar da za su iya bashi shawara.
“Tun da gwamna bai ba wa na kusa da shi dama ko fuska su ba shi shawara ba, to kuwa lallai haƙƙi ya rataya a kan duk mai kishin Kano ya faɗa masa gaskiya.
“Mai girma Gwaman Kano Abba K. Yusuf sai ka gyara mu’amillar ka da mashawartanka da kuma masu riƙe da muƙaman gwamnati.
“Zancen da mu ke ji shi ne kwamishina sai ya yi wata da watanni ya na son ganin gwamna kan abu mai muhimmanci amma ya kasa gani ko magana da gwamna ta waya. Wannan bai kamata ba, domin kuwa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
“Binkicen da na yi ya nuna cewa Mallam Daurawa ya yi yunƙurin ganin gwamna don tattaunawa da shi kan matsalar Murja Kunya amma gwamna bai ba shi dama ba. Ya yi yunƙurin yi masa bayani ta waya, nan ma abin ya ci tura.
“Sukar da gwamna ya yi wa Hukumar Hisba jiya a bainar jama’a kamar mutum ne ya daɓa wa kansa wuka, domin kuwa gwamnatinsa ya zaga. Kuma dole jama’a su ce saboda Hisba ta kama Murja Kunya gwamna ya yi wannan magana — domin kuwa a lokacin da Hisba ta ke kama masu baɗala ta na jefa su a bayan mota gwamna bai ce uffan ba sai bayan an kama wannan yarinya.
“Duk mai hankali ya san cewa akwai hannun gwamna (ba wani gwamnati, GWAMNA) dumu-dumu a fitar da murja daga gidan yari ba bisa doron doka ba. ‘Yan watannin baya kamar mu haukace saboda ana yunƙurin kawar da gwamnatinka ba bisa doron doka ba, amma abin takaici kai kuma ka yi wa doka hawan ƙawara saboda wata ballagaza bankaura.”, a cewarsa.
Shi kuwa, Fitaccen Lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Barista Abba Hikima Fagge, shawartar Gwamnan ya yi da kada ya karɓi takardar murabus ɗin shugaban na Hisbah.
Ga abin da ya ke cewa, “Ina roƙon gwamnan Kano da ya ƙi karɓar murabus ɗin Mal. Daurawa kuma a zauna a ɗinke wannan ɓaraka. Don Allah.
“Lokacin da AKY ya ci zaɓe, aka kafa transition kwamiti, an saka ni cikin kwamitin shariah wanda a karkashin wannan kwamiti mai ma’aikatu kusan 9, Hisbah ta faɗo. Muna cikin aikin wannan kwamiti sai aka rarrabawa ma’aikatun karkashin yan kwamiti, sai hukumar Hisbah ta faɗo karkashina.
“Wannan ya bani damar yin zuzzurfan binkice akan Hisbah, ayyukanta, matsalolinta da sauran su. Sannan ya bani damar fahimtar irin sakacin da shugabancin Hisbah na wancan lokaci yayi wanda hakan ne yasa ayyukan Hisbah da ƙimarta suka dakushe.
“Amma da zuwan Daurawa, wannan ya chanja. Duk da gaskiyane akwai buƙatar gyara a wasu daga ayyukan Hisbah, amma lallai Mal Daurawa yana kan nuna nagarta da sanin makamar aikin. Kuma daf yake da cin gagarumar nasara.
“Maganganun gwamnan Kano a bainan nasi kuma a dai-dai wannan lokaci da ake ta kai ruwa rana da mutane masu bayyana baɗala ba dai-dai bane. Kuma don Allah ya janye su. Domin bai wuce yin kuskure ya kuma gyara ba. Amma shima Mallam don Allah, ya fahimci aikin Allah ya gaji jarrabawa. Idan an samu damar kuma ya zama babu zubewar mutunci ko ƙima, ayi haƙuri
“Allah ya basu ikon baiwa shaiɗan kunya domin ci gaban Kano. Amin.”, a cewar Lauyan.
Shima shahararren Malamin Addinin nan, Dr. Abdallah Gadon-Kaya, buƙatar Gwamnan ya yi da ya fito ya bawa Malamin haƙuri.