Tsaro

Kano Za Ta Sanya Hannu Wajen Gudanar Da Taro Kan Sha’anin Tsaro, A Arewa

Gwamnatin Kano ta amince da hada guiwa da rukunin kafafen yada labaran Media Trust, da ke wallafa Jaridar Daily Trust, kuma mamallakan Gidan Talabijin na Trust TV da Trust Radio, domin gudanar da taron bunkasa tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

An cimma yarjejeniyar ne a jiya, ya yin da shugaban gamayyar daraktocin kamfanin, Malam Kabiru Yusuf, ya kaiwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ziyara, a gidan Gwamnati.

Ta cikin wani jawabi da ya fitar, mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya bayyana cewar, shugaban rukunin kafafen yada labaran na Media Trust Group ya kaiwa Gwamnan Kano ziyara ne, domin bayyana masa shirinsu na shirya taro kan tsaron jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai, tare da shirinsu na hada guiwa da gwamnatin wajen gudanar da taron, da sauran alámura.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button