KAROTA Ta Kama Magungunan Da Wa’adin Amfanin Su Ya Ƙare, Na Miliyan 30
Hukumar Kula Da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta samu nasarar daƙume magungunan ƙwarin da wa’adin Amfaninsu ya ƙare, tare da wasu Magunguna da kimarsu ta kai Naira Miliyan 30, a Jihar.
Bayanin hakan na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ya fitar, ranar Juma’a, a birnin Kano.
Inda jawabin ya bayyana cewar, hukumar ta samu nasarar yin ram da Motar da ke maƙile da magungunan waɗanda wa’adin Amfaninsu ya ƙare ne, da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis, 24 ga watan Augusta, akan titin Zaria.
“Da farko daman Jami’anmu sun zargi Motar da kwaso kayayyakin laifi, bayan kuma sun ƙaddamar da bincike sai Direban ya basu tsohuwar takardar Waybill, ya kuma tsere ya bar Motar a wurin”, a cewar jawabin.
Ka zalika ya ƙara da cewar, daga cikin magungunan akwai Magnesium Suspension; Painkillers; Amoxicillin; Diclofenac Injections; Ciprofloxacin; Antibiotics; da Dexamethasone, da makamantansu.
Hukumar ta KAROTA dai, ta daɗe ta na nuna bajintar daƙume miyagun ƙwayoyi, da ma magungunan da wa’adin Amfaninsu ya ƙare, tare da miƙasu ga hukumomin da ke da Alhakin kula da fannonin.