Kashi Na Huɗu Na Ɗaliban Kano 150 Da Gwamnati Ta Ɗauki Nauyi Sun Isa Ƙasar India
Rukuni na huɗu na ɗaliban jihar Kano, kimanin 150, da Gwamnati ta ɗauki nauyin karatun Digirinsu na biyu, a fannoni daban-daban, sun isa ƙasar India.
Kimanin Ɗalibai 1,001 ne dai, waɗanda su ka kammala karatun Digirinsu na farko, da daraja ta ɗaya (First Class) Gwamnatin ta Kano ta ɗauki nauyin ƙaro karatunsu zuwa Digiri na biyu, a ƙasashen ƙetare.
Jirgin da ya ɗauki ɗaliban, ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano ne, da misalin ƙarfe 7:30 na safiyar yau (Juma’a), bayan da su ka yi bankwana da Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar, Yusuf Kofarmata, da ƙarin wasu daga cikin muƙarraban Gwamnati.
Sun kuma fara sauka ne a birnin Lagos, kafin ɗorawa da tafiyar tasu zuwa ƙasar India.
Da ya ke jawabi, jim kaɗan bayan tashin ɗaliban, Kofarmata ya ce, rukunin na huɗu da su ka tashi a yau, na daga cikin kimanin ɗalibai 1,001 da Gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin karatunsu na Digiri na biyu, a kakar karatu ta 2023/2024.
Kofarmata, ya kuma ce an zaɓo ɗaliban waɗanda su ka kammala Digirinsu na farko ne, duba da irin ƙwazon da su ka nuna, na kammalawa da daraja ta ɗaya.
Kwamishinan ya kuma ce, ɗaliban za su yi karatu a ƙasashen ƙetaren ne a fannonin da ake matuƙar buƙata, bisa manufar cike wawakeken giɓin da jihar, da ma ƙasa baki ɗaya su ke da shi, a irin waɗancan fannoni.
Bugu da ƙari, ya bayyana cewar, kimanin Ɗalibai 140 ne su ka tashi zuwa ƙasar ta India a rukunin farko, ya yin ƙaddamar da shirin tun a ranar 20 ga watan Oktoba; Sai kuma rukuni na biyu, da ya ƙunshi kimanin Ɗalibai 33, waɗanda su kuma su ka tashi zuwa Jami’ar Musulunci, da ke Uganda.