Kashi Na Uku Na Ɗaliban Kano Sun Tashi Zuwa Indiya
Da safiyar, Juma’a ne, kashi na uku na ɗaliban Kano 1001 da Gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin karatun Digirinsu na biyu, a Jami’o’in ƙasashen ƙetare mabanbanta, su ka tashi zuwa ƙasar Indiya.
Ɗaliban sun tashi ne, daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, da ke ƙwaryar birnin jihar ta Kano, da misalin ƙarfe 7 na safiyar yau.
Inda su ka yi bankwana da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da wasu daga cikin muƙarraban Gwamnati, kafin tashinsu.
Idan za a iya tunawa kuma, a makon da ya gabata ne, rukuni na biyu na Ɗaliban da Gwamnatin Kanon ta ɗauki nauyin karatunsu, su ka tashi zuwa ƙasar Unganda, ya yin da rukunin farko kuwa, su ka garzaya Indiya.
Hakan kuma, na daga cikin ƙudurin Gwamnatin Kanon, na fitar da Ɗaliban jihar zuwa Jami’o’in ƙasashen ƙetare, domin samo ingantaccen Ilimi, da kyakykyawan tsarin rayuwar waɗancan ƙasashe.