Kashim Shettima Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Samar Da Ayyukan Yi
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da tagwayen cibiyoyin OTNI da BPO, bisa manufar bunƙasa samuwar miliyoyin ayyukan yi, a ƙasar nan.
Da ya ke jawabi, ya yin ƙaddamar da cibiyar jiya, a jihar Gombe, Shettima ya ce an ƙirƙiri OTNI ne domin bunƙasa samar da miliyoyin damarmakin Ayyuka, ya yin da a gefe guda haɗuwarsu da BPO zai taka gagarumar rawa wajen bunƙasa amfani da fasaha a harkokin kasuwanci.
Ya kuma ce OTNI ɗin wata alama ce da ke nuni da haɗin kai tsakanin gwamnati da ɓangarori masu zaman kansu.
Bugu da ƙari OTNI ɗin, za ta haɗa kan kamfanonin duniya da ƴan Najeriya masu ƙwazo.
A nasa jawabin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, na jihar ta Gombe, ya ce ƙaddamar da cibiyar BPO ɗin a jihar Gombe, abu ne da zai haifar da cigaban jihar a matakin duniya, tare da bunƙasa kasuwancin jama’ar Najeriya.