Kaso 60 Na Masu Kiwon Kaji A Najeriya Sun Yi Bankwana Da Sana’ar
Shugaban gidan gonar, Obasanjo Farms, Dr Ariyo Eyitayo Olusegun, ya ce kaso 60 na manoman da ke gudanar da sana’ar kiwon Kaji a ƙasar nan, sun watsar da sana’ar, sakamakon halin matsin da ake fama da shi.
Olusegun, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Daily Trust.
A cewarsa kuma, fagen gudane daga cikin manyan ɓangarorin da ke samar da nama, da ƙoyaye a ƙasar nan.
Ka zalika, ya bayyana tashin farashin da kayayyaki su ke yi, a matsayin babban ƙalubalen da su ke fuskanta, duba da cewar ba sa iya ƙara farashin kayayyakin da su ke samarwa, duk kuwa da tsadar da kayayyaki su ka yi, a ya yin da su ke kiwon.
Olusegun ya kuma ce, tuni masu ƙaramin ƙarfin da ke gudanar da sana’ar kiwon su ka yi bankwana da sana’ar, ya yin da masu ƙarfin da ke cikinta kuwa, a koda yaushe su ke gudanar da sana’ar cikin yanayin tangal-tangal.
Sai dai, ya shawarci manoman da su gujewa ƙauracewa kiwon, dan gudun hukunta waɗanda basu ne masu laifi ba a cikin al’amarin.