Kasuwanci

Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya Na Cigaba Da Bunƙasa

Kasuwar hannayen jarin kasar nan, ta fara da labari mai dadi, a makon da mu ke ciki, wanda hakan ke shafar kwarin gwuiwar masu sanya hannayen jari, hakan kuma ya zo ne kwanaki kadan bayan rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Idan za a iya tunawa dai, a ya yin da ya ke gabatar da jawabin rantsuwarsa, Tinubu, ya ce gwamnatinsa ba zata cigaba da biyan tallafin man fetur ba, duba da baya cikin kasafin kudin 2023, ya yin da ya kara da shan alwashin bunkasa kimar sauyin kudin kasa da nufin bunkasa tattalin arziki.

Sai dai, rahoton kasuwar zuba hannayen jari da aka fitar ranar Jumaá, ya bayyana yadda aka samu ribar Naira tiriliyan 1.505, wato kaso 5.22, inda ya tsaya akan Naira tiriliyan 30.349, daga Naira tiriliyan 28.844 da ya ke a baya.

Ka zalika, shima adadin hannayen jarin da ke kan shiyyoyi ya kai 2,764.47, wato kaso 5.22, idan aka kwatanta da 55,738.35, wanda ya yi dai-dai da 52,973.88, da aka kidaya a kasuwancin baya.

Inda jimillar ribar da aka samu cikin shekarar nan ta kai kaso 8.76.

Manyan kamfanonin da karansu ya kai tsaiko dai a kasuwar sun hadarda, Kamfanin MTN Nigeria, Kamfanonin Simintin Dangote, da na BUA, Sai kuma bankuna irinsu Guaranty Trust, Access, UBA, da ma bankin Zenith.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button