Kiran Yajin Aiki Cikin Watanni 9 Da Fara Gwamnatina, Ba Adalci Bane – Tinubu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, da ta kasance mai ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, ya na mai cewar, kiran yajin aiki cikin watanni tara da fara gwamnatinsa ba adalci bane.
Shugaban, ya bayyana hakane a ya yin ƙaddamar da layin dogo, da aka samar a jihar Lagos, ya na mai nuna irin tanadi mai daɗin da gwamnatinsa ke yi wa ƴan Najeriya.
Da ya juya kan ƴan ƙwadago kuwa, shugaban ya ce duk da yadda su ke taƙama da ƴancin da su ke da shi da damarmakinsu, kiran yajin aiki cikin watanni tara da fara gwamnatinsa ba abu ne da za a “aminta da shi ba”.
“Idan kuna son shiga Siyasa ne, to ku jira zuwa 2027; idan kuma ba haka bane, to ku girmama zaman lafiya. Ba ku kaɗaine muryan ƴan Najeriya ba”, a cewarsa.
Kalaman na Shugaba Tinubu kuma, na zuwa ne kwana guda bayan ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta shirya zanga-zanga ta musamman, domin nuna fushinta da halin matsin rayuwar da al’umma ke ciki.
NLC dai, ta tsara gudanar da zanga-zangar ne tsawon kwanaki biyu, amma ta dakatar da ita daga ranar farko.
Ƙungiyar ta kuma ce, za ta tsunduma Yajin Aiki a nan gaba, muddin gwamnati ta gaza shawo kan lamarin.