Zamantakewa

Ko A Bible Babu Annabin Da Ya Auri Mata Ɗaya Kacal – Ɗan Oshoffa

Olatosho Oshoffa, wanda ɗa ne ga Malamin da ya samar da Cocin Celestial ta Kiristocin faɗin duniya, Bilewu Oshoffa, ya bayyana fahimtarsa kan tsarin Auren Mace fiye da ɗaya a Coci, ya na mai cewa, Coci bata haramta hakan ba.

Olatosho, ya bayyana hakan ne, a Ketu, da ke jihar Lagos, yayin da ya ke kare yawan Iyalan da Mahaifinsa ya ke da su, yana mai cewa, ‘babu wani Annabi mai Mata ɗaya, da ya zo a Bible’.

“Shin zan iya sanar da ku wani abu… ?, Paul shawara kawai ya dinga bayarwa. Ku faɗa min, a cikin Bible, wanne Annabin Allah ne ya ke da Mace ɗaya kawai ?, Ku yi bincikenku, sai ku faɗamin”, a cewarsa.

Marigayi Oshoffa, ya rasu ya bar mata 13, da Ƴaƴa 53, wanda tsarin rayuwarsa ke cigaba da yamutsa hazo, duk kuwa da kasancewarsa guda daga cikin Jagororin Manyan Cocinan Najeriya.

Sai dai, a matsayin Tosho, na ɗan ƙaramin Oshoffa, shi ma yayi kira da a yi watsi da wannan tunani, ya na mai cewa, duk da kasancewar Marigayi Babansa tuntuni ya na da Mata uku, Ubangiji ya sahale masa samar da tafiyarsa, tun tsawon shekaru 76 da su ka gabata.

“Ina da tabbacin cewar, a shekarar 1947, da da wanda yafi cancanta ya jagoranci CCC, ba za a zaɓi Oshoffa ba.

“Amma saboda babu wanda ya kai shi, shi kaɗai Ubangiji ya bawa ikon samar da CCC, duk kuwa da kasancewar ya na da mata uku. Saboda haka, waɗanda su ke ƙalubalantar mahaifina akwai buƙatar su san cewa, bai aikata wani kuskure ba.

“Ya Aure su (Matansa), kuma dukkanninsu sun kasance a ƙarƙashin inuwarsa. Amma a yau, ana ganin Mazaje masu Mata ɗai-ɗai kacal ne, na Ubangiji.

“Wanne ya fi ?, Ina mai sanar da ku cewar, da Ubangiji ne Alƙali kan yawan Mata, kafin shirin turo Limanin Coci, to da bai cancantar da Mahaifina ba, domin ya na da Mata uku, kafin Ubangiji ya kira shi”, a cewarsa.

Da aka tambaye shi, kan yadda Mahaifinsa ya ke samun kusanci da tarin Iyalansa, sai ya ce, Mahaifinsa bai taɓa horas da yaran da ba Mahaifiyarsu ɗaya ba.

“Bari na faɗa maka wani abu ɗan uwana. Ya yin da Mahaifina ya ke doron duniya, ya na haɗa mu, ya sanar da mu cewar, kada ku ce ku Ƴaƴan wata daga cikin Matana ne. Kawai ku sanar da kanku cewar, ku Ƴaƴan Oshoffa ne.

“Kaga hakan ya na nuna yadda yake ƙoƙarin wanzar da soyayya a tsakaninmu. Saboda haka bama ganin kawunanmu a matsayin Ƴaƴan Iyayenmu Mata, kawai muna ganin kanmu ne a matsayin Ƴaƴan Oshoffa. Haka muke lokacin da (Oshoffa) ya na da rai, haka kuma muke bayan mutuwarsa.

“Ko a yau, sauran Matan Oshoffa da Mahaifiyata ta girma, ina cigaba da ɗaukarsu a matsayin Iyaye, saboda soyayyar da Mahaifinmu ya yi amfani da ita, wajen haɗa kanmu. Saboda haka muna cigaba da kasancewa tare a matsayin Ƴaƴan Oshoffa”, a cewarsa.

Da aka juya kan batun rikicin shugabancin da ya mamaye Cocin ta Celestial kuwa, Malamin ya ce waɗan nan rikice-rikice sun kunno kai ne, bayan rasuwar wanda ya samar da Cocin. Amma ya na fatan matsalolin za su kawo ƙarshe, a nan kusa.

Ya kuma bayyana Yayansa, Rev. Emmanuel Oshoffa, a matsayin Jagoran Cocin.

“Yanzu kam, rikicin wanda zai jagoranci Cocin ya ɓarke bayan fakuwar wanda ya samar da ita, kamar yadda Jesus ya faku.

“Haka tarihi ya bayyana mana cewar, ya faru da Cocin Katolika ma, lokacin da ta samu mabanbantan masu son shugabantarta. Amma a yau, shugabansu ɗaya ne kawai, bayan shafe tarin ƙarnuka.

“Hakan kuma ya zo dai-dai da halin da CCC take ciki, bayan rasuwar wanda ya samar da ita, matsaloli da dama sun ɓarke. Kuma shugabanta ya na fuskantar ƙalubale ne irin wanda na Cocin Catholic ya fuskanta.

“….Amma har zuwa yau, shugaban da aka fi amincewa da shi a CCC a duniya baki ɗaya, shi ne Ɗan wanda ya samar da ita na farko, Yayana, Rev. Emmanuel Oshoffa, wanda ya ke zaune a Imeko, Ketu, da Makoko, waɗanda su ne helikwatocin Cocin”, a cewarsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button