Ko Da Gaske Yawan Cin Wake Na Sanya Gajerun Mutane Yin Tsawo ? – Binciken Masana
Masana harkar cimaka sun bayyana cewar, yawan cin wake ba zai iya sanya yaran da Iyayensu gajeru ne su yi tsawo ba, duba da cewar ko kaɗan babu sinadarin yin tsawon a jikinsu.
Masanan sun ce, wake shi ne abincin da ke gina jiki mafi araha, amma sam yawan cinsa ba zai iya sanyawa yaran da ke da gajerun Iyaye su yi tsawo ba, saboda sam-sam basu da sinadarin yin tsawon a halittarsu.
Ka zalika, sun ƙara da bayyana cewar, ko kaɗan waken ma bashi da wani sinadari da ke haɓɓaka girman jiki, domin saurin girman yara ya na da alaƙa ne da, Gado, Nau’in Abincin Da Su Ke Ci, Muhallin da su ka tsinci kansu, da ma samun hutu.
Bugu da ƙari sun ce, a madadin samun tsawo, yawan amfani da waken a matsayin Abinci, kawai zai sanya teɓa da ƙaton timbi ne.
Wani sakamakon bincike da fitaccen masanin kimiyyar nan ɗan ƙasar Amurka, Springer Nature, ya wallafa a Mujallar German-British Academic, ya bayyana cewar kaso 60 zuwa 80 na banbancin tsawon da ake samu a tsakanin jama’a, ya na da alaƙa ne da gado.
Sai kuma kaso 20 zuwa 40 ɗin da ya ce, ya shafi Muhalli ne, da Cimaka.