Wasanni

Kofin Afirka: Babu Kocin Najeriya Ko Ɗaya A Jerin Masu Horaswa 85 Da CAF Ta Fitar

Babu mai horaswa daga Najeriya ko guda ɗaya, a jerin masu horaswa guda 85 da hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afirka ta fitar, domin basu horo a shirye-shiryen gudanar da gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Afirka, da za ta gudana a ƙasar Cote d’Ivoire, a shekarar 2024.

Ƙasashen Egypt da Algeria da ke Arewacin Afirka ne dai su ke da masu horaswa mafi yawa da ke cikin wancan rukunin sunaye.

CAF, ta kuma bayyana sunayen ne ta cikin wani kundi da ta fitar, mai taken, “Sunayen Masu Horaswar da aka zaɓa, domin halartar horo gabanin gasar AFCON”, sunayen masu horaswar kuma sun fito ne daga ƙasashe sama da 26 da ke nahiyar Afirka.

Abin al’ajabi a cikin fitar da waɗannan sunaye dai, bai wuce rasa Kocin Najeriya ko da guda ba, a jerin 43, wanda hakan ke alamta yiwuwar yadda Najeriyar ka iya rasa ko da kujera guda, a jerin masu ruwa da tsakin gasar, wacce za ta gudana a shekara mai kamawa.

Ƙasashen Egypt da Algeria ne kuma su ka fi yawan masu horaswar da aka zaɓa ɗin, inda kowaccensu ta ke da guda Uku, ya yin da ƙasashen Morocco da Mauritania, tare da Mauritius su ke da guda bibbiyu.

Sauran ƙasashen da ke cikin jerin sunayen, sun haɗar da: Gabon, Ghana, Benin, Congo, Somalia, da makamantansu.

Ka zalika, ƙasashen Morocco, Kenya, Cote D’Ivoire, Algeria, Egypt, da Afirka ta Kudu, su na da sunayen mataimakan masu horaswa guda bibbiyu.

Baya ga haka, an ɗauko Alƙalan kula da na’urar VAR guda huɗu daga: Mauritius, Afirka ta Kudu, Morocco da Egypt.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button