Wasanni

Kofin Afirka: Tawagar Kiriket Ɗin Najeriya Za Ta Fafata Wasa A Daren Yau

Bayan disashewar fatanta na samun cancantar zuwa gasar Kiriket ta ICC T20 ta shekarar 2024, sakamakon fuskantar rashin nasara da ta yi har karo 9, bayan wasan da su ka fafata da Uganda a ranar Litinin, Fatan da ya ragewa Najeriya a yanzu bai wuce samun nasara a wasan neman cancantar buga gasar Kofin ƙasashen Afirka na wasan Kiriket ɗin wanda za su fafata tare da ƙasar Zimbabwe a yau ba.

Bayan nasara da makin da Najeriyar ta samu a wasannin farko da na biyu, a yanzu tawagar ƙasar na buƙatar sake samun nasara , domin shallake ƙasar Uganda wacce ke da gagarumin maki.

A yanzu dai, tawagar za ta fafata da Zimbabwe ne, wacce ita ma ta ke da yiwuwar buga wasa da tawagar ƙasar da ke karɓar baƙuncin wasan ta Namibia, idan ta doke Najeriyar.

Najeriya na a mataki na huɗu a teburin gasar ne a halin da ake ciki, inda ta ke ɗauke da kimanin maki uku, kuma take saman ƙasashen Rwanda da Tanzania, ya yin da Zimbabwe ke a matsayin ta uku da maki hudu, a wasanni bibbiyu dukkanninsu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button