Wasanni

Kofin Duniya 2024: NCF Ta Fitar Da Sunayen Ƴan Wasan Da Za Su Wakilci Najeriya A Wasan Neman Cancantar Kiriket Ta Mata

Hukumar kula da wasannin Kiriket ta ƙasa, ta fitar da jerin sunayen ƴan wasa 14, da za su wakilci a ƙasar nan a wasannin neman cancantar buga gasar kofin duniya na shekarar 2024, da zai gudana daga ranar 7 zuwa 17 ga watan Disambar da mu ke ciki, a ƙasar Uganda, ya yin da wasu ƙarin ƴan wasa biyu za su kasance a jerin masu jiran ko ta kwana.

Shugaban tawagar masu horas da ƴan wasan, Leke Oyede, shi ne ya bayyana sunayen jerin ƴan wasan, bayan gayyatar ƴan wasa 18 zuwa babban sansanin horas da ƴan wasan kiriket da ke Benin, na jihar Edo.

Ƴar wasa mafi daɗewa a tawagar wacce kuma ke matuƙar nuna ƙwazo, Blessing Etim, ita ce za ta jagoranci tawagar a matsayin Captain, inda sauran fitattun ƴan wasan da ke cikin tawagar su ka haɗarda: Sunday Salome; Esther Sandy; Lucky Piety; Victory Igbenedion; Favour Eseigbe da ƴar wasa Christabel Chukwuonye, da ma wasu ƙarin ƴan wasan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button