Kofin Shugaban Ƙasa: Kano Pillars Za Ta Fafata Da Doma United, A Zagayen 32
Jadawalin zagayen 32 na gasar Kofin Shugaban Kasa, na shekarar 2024, wato President Federation Cup 2024, ya kasance mai matukar ban kaye, bayan da aka tsara gwabzawar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Doma United ta jihar Gombe, a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun da mu ke ciki, a budadden filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, da ke babban birnin tarayya Abuja.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars, mai lakabin ‘Sai Masu Gida’ dai, ta cire Enugu Rangers daga wasan bayan da ta jefa mata kwallaye 6 da 5 a bugun fenaretin zagayen 64, bayan da aka karkare wasa kunnen doki 1 da 1, a filin wasa na Bwari Township, da ke Abuja, da nufin samun nasarar kaiwa zagayen yan 32.
An fitar da jadawalin wasannin zagayen 32 din ne dai a jiya, inda a cikin jadawalin aka tsara fafata wasan tsofaffin zakarun gasar NPFL na Plateau United da Sunshine Stars, a tare.
Dukkannin bangarorin biyu, za su yi kokarin fitar da abokanan burminsu, da zarar an fara fafata asan a ranar 22 ga watan Mayu.