Kotu

Kotu Ta Ɗaure Matashi Watanni 4 Bayan Samunsa Da Laifin Satar Doya

A ranar Litinin ne, Kotun Dei-Dei 1, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta yankewa wani matashi mai shekaru 22, Felix Adams, hukuncin ɗaurin watanni huɗu, a gidan ajiya da gyaran hali, bayan samunsa da laifin satar doyar kudu, a gonar makaranta.

An kuma gurfanar da Adams ɗin a gaban Kotu ne, bisa tuhumar aikata sata, da mallakar kaya ta mummunar hanya.

Lauyan mai ƙara, Mr Chinedu Ogada, ya ce wanda ya ke tsayawa mai suna, Tonushi Chibwa ne ya kai matashin ofishin rundunar ƴan sanda na Dutse Alhaji, tun a ranar 19 ga watan Oktoban shekarar da mu ke ciki.

Lauyan mai ƙarar, ya kuma ce, bayan tsaurara binciken ƴan sandan ne kuma, sai wanda ake zargin ya furta cewar, ya sato doyar ne a gonar makarantar, Government Day Secondary School, Dutse Alhaji.

Matashin ya kuma saci doyar ne da nufin zai sayar, amma aka yi nasarar cafke shi kafin aikata hakan.

Ogada ya ce, laifukan sun saɓa da tanadin sashe na 348, da 287 na kundin Penal Code.

Da ya ke zartar da hukunci, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Saminu Suleiman, ya aike da mai laifin gidan gyaran hali na tsawon watanni huɗi, ko zaɓin biyan tarar Naira 10,000.

Kotun ta kuma ja kunnensa kan gujewa aikata dukkannin wani nau’i na laifi, bayan karɓar hukuncinsa na yanzu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button