Kotu Ta Ɗaure Wanda Ya Tsayawa Mai Laifi Watanni 6, Saboda Gaza Gabatar Da Wanda Ya Tsayawa
Babbar Kotun Majistiri, da ke jihar Kaduna, ta yankewa wani mutum mai suna, Jacob Timothy, da ke da shekaru 47 hukuncin ɗaurin watanni 6 a gidan gyaran hali, sakamakon gaza gabatar da ɗan uwansa, wanda ya tsayawa domin Kotun ta bada belinsa.
A ranar Talata, Alƙalin Kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bada umarnin tasa ƙeyar Timothy ɗin, a dalilin karantsaye ga shari’a.
Wannan hukunci kuma, ya zo ne bayan gabatar da zaman Kotun har karo uku, ba tare da mutumin ya gabatar da ɗan uwan nasa da ya tsayawa ba.
Sai dai, Kotun ta bawa mutumin zaɓin biyan tarar Naira 25,000 a madadin ɗaurin.
Tunda farko dai, Timothy ɗin ya tsayawa ɗan uwansa, Caleb, mai shekaru 38, wanda ake zargi da ji wa wani rauni ne domin bada belinsa.
Kuma Caleb ɗin, ya yagawa wani mutum mai suna, Gabriel William kayansa ne, tare da watsa masa Ruwan zafi, bayan da su ka samu saɓani akan canjin Naira 150.
Laifin da Tamothy ɗin ya yi, na gaza gabatar da shi kuma, ya saɓa da dokar Penal Code ɗin jihar ta Kaduna, ta shekarar 2017.