Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum, Bayan Samunsa Da Laifin Zamba A Cinikin Fili
Kotun Shari’ar Musulunci, da ke Kwana Huɗu, a jihar Kano, ta aike da wani mutum mai suna, Usaini Ayuba, ɗan asalin ƙaramar hukumar Ungogo, gidan gyaran hali tsawon watanni tara, bayan samun da laifin zamba, wajen sayar da fili.
Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara, Aliyu Abidin Murtala, ya bayyanawa Kotun cewar, wanda ake zargin ya karɓi kuɗi kimanin Naira 250,000 ne a hannun wata Matar Aure, bayan da ya yi mata alƙawarin saya mata Fuloti, amma daga lokacin da ya yi hafzi da kuɗin, sai ya garƙame layukan wayarsa, tare da yunƙurin ficewa daga ƙasar, kafin samun nasarar yin ram da shi, da aka yi.
Bayan amsa laifinsa kuma, sai Alƙalin Kotun, Malam Nura Yusuf ya aike da shi gidan gyaran hali na tsawon watanni tara, ko zaɓin biyan tarar Naira 50,000 tare da mayarwa wacce ya zalinta kuɗaɗenta.