Zamantakewa

Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum Bisa Zargin Yi Wa Ɗan Uwansa Fyaɗe

Kotun sauraron shari’un Iyalai ta jihar Ondo, da ke da matsuguni a Akure, babban birnin jihar ta Ondo, ta bada umarnin tsare wani mutum mai suna, Pelumi Folorunsho, bisa zarginsa da yi wa ɗan uwansa fyaɗe.

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar ne dai, su ka yi ram da mutumin, bisa zarginsa da aikata luwaɗi akan wani yaro mai shekaru takwas kacal a duniya, a wani gida mai lamba 3a, Layin Odige, da ke yankin NEPA, a birnin Akure, tun a ranar 16 ga watan Satumban da mu ke ciki.

Maƙwabcin wanda ake zargin ne kuma, ya kama shi a dai-dai lokacin da ya ke aikata wannan ta’asa.

An kuma gurfanar da Pelumi, a gaban kotun sauraron shari’un Iyalai ne, bisa zargin aikata laifi guda.

A cewar ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Mr Martins Olowofeso, Wanda ake zargin ya aikata wannan laifi ne, a ranar 16 ga watan Satumban 2023, da misalin ƙarfe 3 na yammaci, a gidansu, inda ya ƙara da cewar, fyaɗen da matashin ya yi wa wannan ɗan uwa nasa ya haifar masa da rauni.

“Kai, Pelumi Folorunsho, a ranar 16 ga watan Satumban 2023, da misalin ƙarfe 3 na dare, a gida mai lamba 3a, Odige, NEPA Area, da ke Akure, a jihar Ondo, ka ci zarafin yaro mai shekaru takwas a duniya, ta hanyar cusa azzakarinka a cikin duburarsa, wanda hakan gagarumin laifi ne, da sashe na 3(1) (a) na dokar VAPP ta Ondo, ta shekarar 2021 ya yi tanadin hukuncinsa”, a cewar ɗan sanda mai gabatar da ƙara.

Ya kuma ƙara da cewar, wanda ake zargin ya cire wandon yaron ne, ta ƙarfin tsiya kuma ya cusa mazantakarsa a duburarsa, a lokacin da Iyayensa basa nan.

Da ya ke bayyana matsayarsa, Mai Shari’a F.A Aduroja, ya bada umarnin tsare wanda ake zargin a ofishin rundunar ƴan sanda, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na ƙarshe.

Ya kuma umarce shi da ya dinga gudanar da aikin gyaran daji, a ofishin rundunar ƴan sandan, har na tsawon makonni biyu, inda ya ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Oktoban 2023 da mu ke ciki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button