Kotu

Kotu Ta Aike Da Jami’in EFCC Na Bogi Gidan Gyaran Hali

Kotun sauraron ƙarararraki na musamman da ke Ikeja, a jihar Lagos, ta aike da wani mutum gidan gyaran hali, har na tsawon shekara guda, a ranar Laraba, bayan da ta same shi da laifin ayyana kansa a matsayin Jami’in hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, tare da damfarar kuɗaɗen da kimarsu ta kai Euro €45,000.

Mai shari’a Mojisola Dada ce dai, ta aike da mutumin mai shekaru 30 gidan na gyara halinka, bayan samun sa da aikata laifukan sojan gona, da mallakar takardun bogi, da ma damfarar €45,000, kamar yadda hukumar da ta gurfanar da shi, ta zarga.

Ofishin hukumar EFCC na jihar Lagos ne dai, ya kama wanda ake zargin, wanda ke sojan gona a matsayin, Axelle Maheiu, Jami’in kula da al’amuran Ilimi na Belgian.

Matashin ya kuma aikata waɗannan laifuka ne ta hanyar yanar gizo.

An kuma gurfanar da shi a gaban kotun ne, tun a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.

Clinton, ya ce sun sha yin wasan ɓuya da masu bincike kan laifin nasa, kafin daga bisani su ka yi amfani da hanyoyin fasaha wajen yin ram da shi, a ranar 18 ga watan Oktoban 2022 da ta gabata, a gida mai lamba 46, da ke Layin Atoke Gbadebo, a Isherin jihar Lagos.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button