Kotu

Kotu Ta Bada Belin Ɗan Jaridar Da Ya Ci Zarafin Matar Ɗan Uwan Gwamna

A yau (Alhamis) ne, babbar kotun tarayya, da ke Abuja, ta bada belin ɗan jaridar nan, Mawallafin jaridar yanar gizo ta CrossRiverWatch, Agba Jalingo, kan zambar kuɗi har Naira 500,000, tare da mai tsaya masa guda ɗaya, wanda shi ma zai ajiye kwatankwacin wannan kuɗi.

Ana tuhumar Jalingo ne dai, da laifin ɓata sunan, Elizabeth Àyade, wacce mata ce ga Frank Ayade, da ke zama ɗan uwan Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade.

Ta cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/565/2022, an zargi ɗan jaridar da wallafa wani rubutu da ke kamanceceniya da cin zarafi, ko taɓa muhibbar Elizabeth ɗin, wanda kuma hakan ya saɓa da sashe na 24 (1) (b) na kundin manyan laifuka, na shekarar 2015.

Jalingo dai, ya yi shura a fagen wallafa labaran bogi, da ke da alaƙa da cin zarafin Elizabeth Ayade ɗin.

Idan ba a manta ba dai, ko a shekarar 2022 ma, sai da Elizabeth ɗin ta buƙaci Jalingo ya goge wani rubutu da ya wallafa, wanda ta ke ganinsa, a matsayin cin zarafinta.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button