Kotu Ta Bada Umarnin Ƙwace Gidaje 324 A Kano
A jiya (Laraba), hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta ce ta samu izinin ƙwace gidaje kimanin 324, daga kwamitin amintattu na kuɗaɗen fanshon jihar Kano.
Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, shi ne ya bada wannan umarni, ya yin da ya ke yanke hukunci kan buƙatar hukumar EFCC.
EFCC dai, ta buƙaci kotun ne da ta bata izinin ƙwace kadarorin, bayan da ta yi zargin cewar kwamitin amintattun asusun kuɗaɗen gajiyayyun ya mallake su ne ta hanyar da bata dace ba.
Daraktan yaɗa labaran hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, a ranar Laraba, ya bayyanawa Jaridar PUNCH cewar, kayayyakin da kotun ta amince a ƙwace sun haɗar da, Gidaje 168 da ke Sheikh Jafar Mahmud Adam, Bandirawo City, Kano; da Gidaje 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara (Amana City), Kano, sai kuma Gidaje 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City, Kano.