Kotu

Kotu Ta Bada Umarnin Yanka Wani Zakara, Saboda Yawan Cara, A Kano

Kotun Majistiri da ke gidan Murtala, a birnin Kano, ta umarci wani mutum mai suna, Isyaku Shu’aibu, da ke zaune a unguwar Ja’en (Sharada Phase III, da ya yanka Zakaransa.

Wannan umarni kuma, na zuwa ne, bayan da Maƙwabcinsa mai suna, Malam Yusuf Muhammad Ja’en, ya shigar da ƙara a gaban Kotun, kan cewar Zakaran ya na shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci, da yawan Cara.

Kuma ko da aka karantowa wanda ake ƙarar zargin da ake wa zakaran nasa, sai ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara, kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday”, don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

Alƙaliyar Kotun, Mai shari’a Halima Wali, ta amince da wannan buƙata, inda ta umarce shi da ya killace Zakaran, tare da yanka shi, a ranar Juma’a mai zuwa, wato ranar “Good Friday” ɗin, kamar yadda ya buƙata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button