Kotu

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Daga Ɗaukar Mataki, Akan Makarantu Masu Zaman Kansu

Babbar Kotun jihar Kano, ta dakatar da Gwamnatin jihar, daga ɗaukar kowanne irin mataki, akan Makarantun Firamare, da Sakandire masu zaman kansu, har sai ta saurari ƙarar da aka shigar gabanta.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Nasiru Saminu, shi ne ya bada wannan umarni a ranar Alhamis, bayan shigar da buƙatar hakan da Lauyan masu ƙara, Barista AbdulHafees D. Khalid ya yi, a gaban Kotun.

Waɗanda su ka maka Gwamnatin Kanon a gaban Kuliya dai, sun haɗarda, Kwamitin Amintattu na Makarantun Islamiyyu na zamani na ƙasa; Kwamitin amintattu na ƙungiyar mamallaka makarantu masu zaman kansu na jihar Kano; Kwamitin amintattu na mamallaka makarantu masu zaman kansu na ƙasa, reshen jihar Kano; Kwamitin amintattu na masu makarantu masu zaman kansu a Najeriya, reshen Kano; Da kuma Kwamitin Gamayyar mamallaka makarantu masu zaman kansu.

Ya yin da waɗanda ake ƙara kuwa, su ka haɗarda: Gwamnatin jihar Kano; Gwamnan Kano; Atoni Janar; Hukumar kula da makarantun sa kai da masu zaman kansu ta Kano; da Comrade Baba Abubakar Umar.

Kotun ta kuma bada umarnin dakatar da waɗanda ake ƙarar, musamman ma wanda ake ƙara na 5, daga ɗaukar dukkannin wani mataki, har sai Kotu ta saurari ƙarar.

Inda kuma Kotun ta sanya ranar, 21 ga watan Nuwamba, domin fara sauraron shari’ar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button