Kotu Ta Haramtawa Gwamnatin Kano Bincikar Badaƙalar Ganduje
Babbar Kotun Tarayya, da ke Kano ta bada umarnin haramtawa kwamitocin jihar guda biyu, da Gwamnatin Kano ta kafa domin binciken tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, gudanar da binciken.
Idan mai bibiyar Rariya Online zai iya tunawa dai, a watan da ya gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamitocin shari’a guda biyu, da za su yi aikin binciken ɓarnatar da dukiyoyin al’umma da gurɓatacciyar siyasa, a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023, lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, wanda a yanzu ya ke riƙe da muƙamin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Tuni kuma, Kwamitocin ƙarƙashin jagorancin, Zuwaira Yusuf da Faruk Lawan su ka fara gabatar da zamansu.
Sai dai, ta cikin buƙatar wucin gadin da Ganduje ya nema a gaban Kotu, ya yi ƙarar Atoni Janar na jihar Kano, Hukumar Haraji, tare da Hukumar Shari’a (NJC).
Da ya ke bada umarnin, Mai Shari’a S.A. Amobeda, ya amince da dukkannin buƙatu biyun da Ganduje ya miƙa masa, inda kotun ta haramta musu gudanar da ayyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kallafa musu, har sai Kotun ta saurari shari’ar.
Kotun, ta kuma sanya ranar 28 ga watan Mayun da mu ke ciki, a matsayin ranar da za ta fara sauraron shari’ar.