Kotu Ta Sake Dakatar Da Ƙungiyar Ƙwadago Daga Shiga Yajin Aiki
Kotun masana’antu da ke Owerri, babban birnin jihar Imo, ta sake fitar da umarnin dakatar da ƙungiyar ƙwadago daga tsunduma kowanne irin nau’i na Yajin Aiki, a jihar, har sai Kotun ta bayyana matsayarta.
Kotun ta kuma yi gargaɗi kan bijirewa wannan umarni, ta na mai cewar, zai iya jawowa ƙungiyar fuskantar fushin hukuma.
Mai Shari’a N C S Ogbuanya, shi ne ya bada wannan umarni, ranar Juma’ar da ta gabata, bayan da ya ji ta bakin Lauyoyin ƙungiyar ƙwadago da na Gwamnatin jihar, tare da buƙatar su sasanta junansu.
Waɗanda ake ƙara a cikin ƙunshin tuhumar dai sun haɗar da, ƙungiyar ƙwadago, da Sakatarenta, Comrade Emmanuel Ugboaja, sai ƙungiyar ƙwadago ta masana’antu masu zaman kansu (TUC) da Sakatarenta, Comrade Nuhu Toro.
Ya yin da Atoni Janar na jihar ta Imo, tare da Gwamnatin jihar su ke a matsayin masu ƙara, a shari’ar mai lamba NICN/OW/41/2023.
Bayan kuma jin ta bakin dukkannin ɓangarorin guda biyu, kotun ta sanya ranar 30 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ƙarar.
Wannan umarni da kotun ta bayar dai, zai sanya dukkannin wani yunƙurin yajin aiki da ƙungiyar ta NLC za ta yi a jihar, ya kasance haramtacce.